Gwamnatin Nijeriya ta gabatar da kasafin kudinta na 2015.
Wakiliyarmu a Abuja Madina Dauda ta ce Ministar kudin kasar Madam Ngozi Okonjo Iweala ce ta gabatar da kasafin kudin a madadin Shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Da ta ke wa manema labarai bayani, Ngozi Okonjo Iweala ta ce wajen yanke shawarar Gwamnatin Nijeriya ta yi la’akari da al’amarin da ke tafe, da kuma kasancewar ta na tunanin hako gangar mai miliyan 2.2 a rana guda, kuma ta na tunanin cike gibin kasafin kudin ne daga kudaden shigar da za a samu daga bangarorin da ba na mai ba.
Ta ce an rage kiyasin bunkasar tattalin arzikin kasar ne daga 6.3 zuwa 5.5% kuma shi ne ma’aunin tattalin arziki mafi aminci a duk duniya. Kasafin ya zo ne a daidai lokacin da bangarorin gwamnati ke shirin tsuke bakin aljuhunta saboda faduwar farashin mai a duniya.
Abdulmumini Jibrin, shugaban Kwamtin Kula da Kasafin Kudi a Majalisar Wakilai. Ya ce da farko an kiyasta kudin gangar mai guda akan dala 78, to amma saboda halin da ake ciki yanzu an mai da shi kasa a yanzu zuwa dala 65. Saboda haka za a zauna a dubi abin da ya dace.
Madina ta kara da cewa wannan na nufin Kenan akwai babban gibi a kasafin kudin na jimlar Naira miliyan 800,000 ko kuma 20% saboda faduwar kudin mai.
Sanata Kabiru Gaya ya yi takaicin yadda wannan karon ma Shugaba Goodluck Jonathan ya ki halartar Majalisar, ya tura Ministar Kudi kamar yadda ya yi bara. Y ace shi ya kamata ace a zo don a mai tambayoyi kan yadda ya aiwatar da kasasfin bara.
Bayan gabatar da kasafin kudin sai Majalisar ta fara hutu na har zuwa 13 ga watan Janairun shekarar gobe.