Bayan sun kammala muhawara akan daftarin shugaban masu rinjaye a majalisar yayi karin bayani akan gyare-gyaren da suka yi.
Gyare-gyaren sun kai saba'in da wani abu. Akwai wadanda suka yadda dasu akwai kuma wadanda suka yi watsi dasu bisa ga ra'ayoyin al'ummar Kano da majalisar ta saurara.
Sun amince da tsarin yadda ake gudanar da kananan hukumomi. Sun yadda cewa hukumar zabe ta jiha ta cigaba yadda take. Sun amince da gagarumin rinjaye akan 'yancin majalisun dokoki domin su samu damar taimakawa dimokradiya yadda ya kamata.
Akan amincewa da 'yancin majalisun dokoki da kuma kin ba kananan hukumomi 'yanci tamkar son kai ne, sai shugaban masu rinjaye yace basu hana shugabannin kananan hukumomi ba. Amma a dimokradiya majalisar jiha ita ce tushe. Idan bata tsaya ba dimokradiya ba zata dore ba domin ba zata zauna da gindinta ba.
Batun hukumar zabe ta jiha na cikin abubuwan da suka fi daukar hankalin jama'a. Majalisar ta dauki matsayin cewa hukumar zaben jiha ta cigaba da zama cikin kundun tsarin mulki.
To amma akwai wasu 'yan majalisar da suke ganin ya fi a ce hukumar zabe ta kasa wato INEC ita ce take gudanar da zaben kananan hukumomi sabili da zai fi ba mutane kwanciyar hankali da kara amincewa da zaben. A nasu ra'ayin babu yadda za'a ce gwamnan jiha shi zai nada hukumar zabe ya bata kudi, ya sa ranar zaben kana a yi zaton jam'iyyarsa ba zata lashe zaben ba.
Ga karin bayani.