Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ba Ta Tsiyace Ba - inji Ministan Kudi


Wata turakata a wani gona a Najeriya.
Wata turakata a wani gona a Najeriya.

Yayin da wasu ke nuna fargabar yiwuwar Nijeriya na cikin matsalar rashin kudi, Ministan Kudin kasar Ambassada Bashir Yuguda ya ce sam Nijeriya ba ta da matsalar kudi.

Ministan Kudin Nijeriya Ambasa Bashir Yuguda ya karyata rade-radin da ake bazawa cewa Nijeriya ba ta da kudi. Ya ce hasali ma gwamnatin Nijeriya na baiwa jihohi karin kudi daga kudin rarar mai da ake kira “Special Allocation On Excess Crude Account.” Y ace don haka maganar Nijeriya ba ta da kudi maganar banza ce kawai.

Ministan ya ce wasu ‘yan hamayya ne da kuma wasu da ba su bincike ke cewa wai Nijeriya ba ta da kudi. Ya ce babu watan da ya wuce da ba a raba kudi ma jihohi ba. Ya ce har yanzu ana baiwa kananan hukumi da tarayya da kuma jihohi kosonsu ba tare da wata matsala ba.

Ministan ya ce akwai hanyoyin samun kudade har kashi hudu akalla: Akwai kudin da ke shigowa daga sayar da mai; akwai wanda ke shigowa daga hukumar Yaki da fasakwabri; akwai kuma wanda ke shigowa daga DPR, wato hukumar da ke kula da matatun main a kasa; sannan akwai kudin da ke shigowa daga harajin da ake dorawa kan kayan da aka sayar.

Minista Yuguda ya ce ai idan aka ce kasa ba ta da kudi to ba za ta iya biyan alabashi ba kuma ba ta iya biyan bashin da ke kanta ko na cikin gida kol na waje, sannan manyan kamfanoni ba za su fito daga kasashen waje su shigo da hannayen jarinsu ba. Don haka, ya ce Nijeriya na da kudi, ba ta tsiyace ba.

Najeriya Ba Ta Tsiyace Ba - inji Ministan Kudi - 4'40"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG