Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijer: Shari'ar Zargin Cin Kudin Tsaro Ta Farfado


Shugaban Kasar Jamhuriyar Issoufou Mahammadou
Shugaban Kasar Jamhuriyar Issoufou Mahammadou

Yayin zagayowar ranar da kasar Nijer da ta Faransa su ka yi asarar wasu sojojinsu, kungiyoyin fafatuka sun sake zaburar da batun shari'ar zargin cin kudin tsaro, wadda su ke zargin ana neman a shiriritar da ita.

A yayinda a jiya, 10 ga watan Disamba aka cika shekara daya da harin ta’addancin da ya hallaka sojoji 71 a Barikin Inates dake iyakar Jamhuriyar Nijer da Mali, wasu kungiyoyin fafatuka sun shigar da kara a wata kotun birnin Yamai don ganin an zakulo masu hannu a badakalar nan ta kudaden makamai a Ma’aikatar Tsaron Kasa.

Kazamar asarar rayukan da aka fuskanta a harin na Barikin Inates ranar 10 ga watan Disamban 2019 wanda ya lakume rayukan dakaru 89 a Chinagoder, iyakar Nijer da Mali, na daga cikin manyan dalilan da suka sa Shugaba Issouhou Mahamadou ya umurci Ministan Tsaro Pr Issouhou Karambe ya gudanar da bincike domin tantance ainahin matsalolin da ke bai wa ‘yan ta’adda damar samun nasara a hare haren da aka yi fama da su a wancan lokaci.

Sojojin Kasar Nijar
Sojojin Kasar Nijar

Binciken ya gano cewa rubdaciki da kudaden makamai da rashin sayen kayakin da suka dace ne ke haifar da wannan mummunan al’amari. Saidai hukunta masu hannu a wannan harkalla ya faskara; dalilin kenan da ya sa kungiyar Rotab Niger da AEC da TLP Natiomale da TLP Internationale suka shigar da kara a kotun Yamai kamar yadda a yanzu haka wasu takwarorinsu na kasar Faransa ke irin wannan gwagwarmaya. Mounkaila Halidou wani daga cikin shika shikan wannan tafiya ya tabbatar da hakan.

Badakalar kudaden makamai wata magana ce da gwamnatin Nijer ta damka rahotonta a hannun alkali mai kare muradun hukuma domin gudanar da bincike a shara’ance. Sai dai watanni fiye da 4 bayan damka wadannan takardu shiru ka ke ji game da batun hukunta masu hannu a wannan ta’asa da ta haddasa salwantar dubban miliyoyin cfa. Dalili kenan ‘yan rajin kare hakkin dan adam suka fara yunkurin farfado da wannan magana, wace a dalilinta wasu daga cikinsu suka ci kason watanni sama da 6 bayan da aka kama su a yayin wata zanga zanga kan batun.

Ga Sule Barma da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00


XS
SM
MD
LG