A jamhuriyar Nijer, kungiyar alkalan shari’a wato SAMAN ta gargadi magoya bayanta da su yi aiki bisa adalci da gaskiya don fayyace abubuwan dake kunshe a rahoton da hukumomi suka gabatar wa mashara’anta, a ci gaba da daukar matakan hukunta wadanda suka handame kudaden makamai a ma’aikatar tsaron kasar, sannan kungiyar ta yi barazanar saka kafar wando guda da duk wanda zai kwatanta tursasa wa magoya bayanta akan aikinsu.
A sanarwar da suka fitar a karkashin inuwar kungiyarsu ta SAMAN kwana daya bayan da gwamnatin Nijer ta damkawa mashara’anta rahoton binciken da ta gudanar a ma’aikatar tsaro inda aka yi ruf da ciki akan kudaden makamai, alkalan shari’a sun bayyana gamsuwa da wannan mataki dake nunin hukumomin kasar sun canza tunani, a cewar sakataren wannan kungiya, mai shari’a Nouhou Aboubakar.
Sau tari kungiyar alkalan shari’a na kokawa a game da shisshigin da fannin shari’a ke fuskanta daga wasu masu fada a ji a Nijer, saboda haka wasu jami’an kare hakkin jama’a ke nuna dari-dari dangane da makomar wannan shari’a ta mahandama kudaden ma’aikatar tsaro inji Nassirou Saidou na kungiar Voix des sans voix.
Kungiyar SAMAN ta jaddada aniyar yin tsayin daka don ganin an mutunta ‘yanci da hurumin da dokokin cikin gida da na kasa-da-kasa suka yi tanadi domin alkalan shari’a akan aikinsu saboda haka ta ja hankalin magoya bayanta su yi gaskiya da adalci.
Alkali mai tuhuma Procureur de la Republique Chaibou Samna, ya shaidawa Muryar Amurka cewa yana kan nazarin wannan rahoton, amma bai yi karin bayani ba.
Cece-ku-ce akan badakalar kudaden ma’aikatar tsaro ta kasa wani abu ne da ya samo asali bayan da a ranar 26 ga watan Fabarairun da ya gabata gwamnatin Nijer ta bukaci ‘yan kwangila da jami’an da aka samu da hannu a wannan harka su maida kudaden da suka handame a maimakon ta gurfanar da su a gaban kuliya.
A saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum