A jamhuriyar Nijer wata kungiyar matasa ta fara ayyukan wayar da kan jama’a ta hanyar kafafen sada zumunta bayan la’akari da yadda wasu ke amfani da kafafen zamani don yada labaran bogi akan cutar COVID-19 yayin da ma’aikatar tsaro ta bada sanarwar gano mutane kusan 100 da suka harbu da wannan cuta.
Kungiyar matasan da ake kira Obsevatoire en ligne de lutte contre le coronavirus OLC, na hangen ganar da matasa masu amfani da kafafen zamani hanyoyin kauce wa kamuwa da cutar ta COVID-19 a matsayin wani bangare na matakan dakile yaduwarta kamar yadda shugaban kungiyar Kabirou Issa ya bayyana.
A ci gaban wannan fafutika, kungiyar ta OLC ta kudiri aniyar yaki da masu yada labaran karya a shafukan sada zumunta a wannan laokaci da wasu ke amfani da wadannan hanyoyin don haddasa rudani a tsakanin jama’a game da cutar coronavirus.
Kimanin kudi biliyan 597 na CFA ne hukumomin Nijer ke fatan kashewa domin yaki da wannan annoba, a saboda haka sabuwar kungiyar OLC ta kudiri aniyar tayar da ‘yan kasa daga barci don ganin sun bayar da gudummuwa a yakin da kasar ta kaddamar kan cutar coronavirus wacce alkaluman ma’aikatar kiwon lafiya ke nunin ya zuwa yammacin jiya Alhamis mutane 98 ne suka harbu, yayin da 5 daga cikinsu suka rasu.
Saurari karin bayani cikin sauti.