A Jamhuriyar Nijar an yi jana’izar wasu ‘yan sanda biyu da suka rasu a sakamakon harin ta’addancin da aka kai a garin Ayorou da ke yankin Tilabery.
Majiyoyi da dama sun bayyana cewa maharan da ke kan babura biyar zuwa shida sun fara ne da bindige wani farar hula a bayan garin Ayorou.
Daga nan suka nufi ofishin ‘yan sanda inda suka yi nasarar halaka ‘yan sanda biyu kuma suka jikkata daya.
Rahotanni sun kara da cewa jami’an tsaron da suka bi sawu sun yi nasarar kashe uku daga cikin wadannan mahara.
Sannan sun kama wasu daga cikinsu kuma ana kyautata zaton farar hular da ‘yan bindigar suka halaka wani abokin tafiyarsu ne da ya tuba.
Bayanai na nunin hadin kan da ‘yan bindiga ke samu daga wasu daidaikun mutane na matukar tasiri wajen yawaitar ayyukan ta’addanci a yankin Tilabery, saboda haka masu rajin kare hakkin jama’a ke jan hankula.
Gwamnan jihar Tilabery, Tijjani Ibrahim Katchiella, ya sanar mana cewa yana kan hanyar zuwa Ayorou saboda tantance zahirin abubuwan da suka faru sanadiyyar wannan hari.
A saurari rahoto cikin sauti daga Nijar.
Facebook Forum