A jamhuriyar Nijar kungiyar lauyoyi ta bayyana damuwa dangane da halin da sha’anin shari’a ke gudana a kasar sakamakon abinda ta kira katsalandan din da ake fuskanta daga bangaren zartarwa.
Sai dai hukumomi sun ce babu kamshin gaskiya a wannan zargi.
Kungiyar lauyoyi a kasar ta zargi hukumomi a bangaren zartarwa da fakewa da kwamitin koli mai kula da sha’anin shari’a wato conseil superieur de la magistrature don canzawa alkalai matsayi ko wuraren aiki ba tare da wata kwakwarar hujjar yin hakan ba. Lamarin da ya sa kungiyar lauyoyi kiran taron manema labarai domin ankarar da hukumomin shari’a rashin cancantar wannan mataki.
Mahamadou Rabiou Oumarou shine mai magana da yawun kungiyar lauyoyi ya sheda wa Muryar Amurka cewa "hakki na farko da kowacce kasa ya kamata ta baiwa mutanenta shi ne shari'a." Ya kuma yi kira ga shugaban kasa da ya kawo masu dauki cikin wannan lamarin.
Sa’o'i kadan bayan korafe-korafen na kungiyar lauyoyi ministan shari’a Marou Amadou ya fitar da sanarwa wace a cikinta ya ruwaito cewa ko kadan babu kamshin gaskiya a abubuwan da ake zarginsa da aikawata.
Ya bayyana cewa, shugaban kasa na da hurumin kiran taron kwamitin koli mai kula da sha’anin shari’a don tantaunawa kan batutuwan da suka shafi wannan fanni kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya yi tanadi saboda haka zancen katsalandan a sha’anin shari’a bai taso.
Saurarri wannan rahoton cikin sauti.
Facebook Forum