Jamhuriyar Nijar ta bi sahun sauran kasashen duniya domin tunawa da ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin yaki da cutar kanjamao ko sida.
Wakiliyar sashen dake kula da cutar kanjamao ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Nijar ita ce ta gabatar da jawabi ma kafofin yada labarai na gwamnati.
Shugabar tana cewa yau ce ranar da aka kebe domin yaki da cutar sida kuma ana tunawa da mutane miliyan saba'in da takwas dake dauke da kayar cutar a duk fadin duniya. Tace haka ma "muna nuna alhininmu da mutane miliyan talatin da biyar da suka rasa rayukansu sanadiyar wannan cutar tun lokacin da ta bayyana zuwa yau", inji wakiliyar.
Ta cigaba da cewa mutane su sani Majalisar Dinkin Duniya ta dauki alwashin gamawa da wannan cutar nan da zuwa shekarar 2030. Tace "muna samun nasarori da dama daga mutanen da shekarunsu suka manyanta amma cutar ta kara habaka wajen yara mata"
A lokacin da aka tattauna dashi Malam Lawali Shebu wani jami'i mai kula da wayewa al'umma kai game da cutar sida a cikin tashar daukan fasinjoji ta garin birnin Konni yace yana da kyau jama'a su maida hankali game fadakarwar da ake yi masu akan cutar.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.