Sidi Muhammad Sidi wani dan jarida a Nijar ya shaidawa Muryar Amurka lamarin da ake ciki a yankin na Cintabaradun.
Ya bayyana cewa mutanen da suka kamu da cutar an kebe masu wuri domin dakile yaduwar cutar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar bada agaji ta Red Cross take cigaba da bada horo da fadakar da al'ummar yankin a kan illar cutar. Hakazalika horon ya shafi malaman makaranta talatin da matasa 'yan aikin sa kai na Red Cross a yankin.
Malam Alagoma Mamman Maiga mataimakin shugaban Red Cross na kasar Nijar gaba daya ya yiwa Muryar Amurka bayani. Ya ambaci wuraren da cutar ta riga ta shiga a yankin. Suna son mutane su gane cutar, illarta da abun da yakamata a yi cikin gaggawa.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.