Lura da yadda ‘yan siyasa suka fara amfani da wasu kalaman da ka iya tasiri a kawunan magoya bayan su wajen tayar da zaune tsaye a wannan lokaci da yakin neman zabe ya kan kama a Nijar.
Wannan ya sa hadin gwiwar CDR kiran taron manema labarai da nufin taka burki ga masu yunkurin shimfida wannan sabon salon siyasa.
Kakakin kungiyoyi ta CDR, Anda Garba Moussa, ya ce kana ganin akwai gugungu na ‘yan siyasa suna yin kalamai na son tada zaune tsaye suna kira ga 'yan kasa a yi tashin hankali idan ba su samu nasara a zabe ba, wannan shi ne abin da suka bayyanawa ‘yan Nijar da kada su saurari irin wadannan batutuwa.
Ya kuma kara da cewa ya kamata duk ‘yan Nijar da su yi aiki da kundin zaben kasar kuma su mutunta dokokin zabe, don su zama abin misali a duniya kuma suna kira ga duk ‘yan Nijar a duk inda suke da kada su saurari batu duk daga inda ya ke idan bana na kwarai ba ne kuma su fito su yi zabe a ranar 21 ga watan Fabrairu.
Shi ma shugaban kungiyar kare hakkin dan adam ta CADDED, Son Allah Dambaji, ya ce zaka kaga babban mutum wanda kai da kanka kasan ya bautawa kasa sai ka zo ka ci zarafinsa kuma ka san yana da jikoki, irin wadannan abubuwan su suka kawo rikicin siyasa a kasar Venezuela.
Dambaji ya kuma kara da cewa ya kamata ‘yan siyasa su yi kira ga magoya bayansu su tabbatar siyasa ba zance cin mutunci ba ce, wadannan abubuwan da suke yi na zage zage su tabbatar an daina shi.
Kasashen duniya sun yabawa Nijar da jama’arta saboda yadda zabubukan watan Disamban 2020 suka gudana cikin kwanciyar hankali.
Wannan dalilin ke nan ake ta jan hankulan magoya bayan Bazoum Mohamed da na Mahaman Ousman su yayyafawa zuciyoyinsu ruwan sanyi don ganin komai na zagaye na 2 na zaben 21 ga watan Fabrairu ya gudana cikin kwanciyar hankali ta yadda wanda ya sha kayi a wannan fafatawa zai rungumi kaddara ko kuma ya bi hanyar da doka ta tsara wajen kalubalantar sakamakon zabe.