A jamhuriyar Nijar malaman makaranta sun fara tserewa daga karkarar Tilabery mai makwaftaka da kasashen Mali da Burkina Faso bayan da ‘yan ta’adda suka kaddamar da kone konen makarantun boko.
'Yan ta'addan sun umurci malamai da su fice daga yankin ko kuma a halaka su, lamarin da ya sa malaman kwantaragi soma wani yajin aikin kwanaki biyu daga yau Alhamis da nufin tada hukumomi daga barci.
Gomman makarantun framary ne aka kyasta cewa ‘yan ta’adda sun cinna wuta a ‘yan kwanakin nan a karkarar Tilabery yankin da a watannin da suka shige tashe tashen hankula suka yi sanadiyar rufe makarantu sama da 100.
Wannan na faruwa ne a wani lokacin da malaman makaranta ke fama da tarin matsalolin rayuwa, mafarin da malaman suka fara yajin aikin kwanaki 2.
A zantawar wakilin Muryar Amurka da shi akan wannan matsala Ministan Ilimi a matakin firamari Dakta Dauda Mahamadou Marthe ya tabbatar da cewa gwamnati na cikin daukar matakan kare malaman makaranta baki daya a yankunan dake fama da hare haren ‘yan bindiga.
Ana su bangare wasu iyayen yara sun fara kiran bangarori su sasanta.
Saurari rahoto cikin sauti daga birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar.
Facebook Forum