Kungiyoyin kare hakkin jama’a a Jamhuriyar Nijer na fannin ilimi suna gargadi ga hukumomin ilimi mai zurfi, da malaman jami’oin, da gwamnati, akan su zauna teburin tattaunawa domin samun masalahar rikicin da ya haddasa tsayawar al’amuran karatu a daukacin jami’o'in kasar.
A bara ne gwamnatin Nijer ta dauki matakin soke zaben shugabannin Jami’o'i don maye gurbinsu da tsarin nadi, wadannan matsalolin su suka janyo ka-ce-na-ce a tsakanin hukumomin ilimi mai zurfi da kungiyar malaman makaranta ta SNECS, wadda a baya bayan nan ta umurci magoya bayanta shiga yajin aikin wata daya, lamarin da ya sa iyayen dalibai suke kiran bangarori su zauna akan teburin sulhu.
Gwamnatin Nijer ta bayyana cewa nada shugabannin jami’o'i ba bakon abu ba ne a Nahiyar Afurka. Irin wannan mataki na bai wa hukumomin damar sanin irin wainar da ake toyawa a jami’o'i mallakar gwamnati.
Kungiyar Malamai ta SNECS ne kallon lamarin tamkar wani katsalandan a harkokin tafiyar da jami’o'i.
Kungiyar kare hakkin jama’a a fannin ilimi, COADE, ta ce mutunta doka ya zama wajibi ga dukkan ‘yan kasa.
Saurari cikakken rahoton Wakilin muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum