A jamhuriyar Nijar hukumar zaben kasar ta tabbatar da daukar matakai domin baiwa jama’a damar su yi rajista a yankunan dake fama da matsalar tsaro sannan hukumar ta CENI ta gargadi ‘yan siyasa su kasance masu bin doka da oda.
Wannan ya biyo bayan ganin yadda ake cigaba da gudanar da rajistar zabe a sassan kasar inda wasu rahotannin ke cewa wasu ‘yan siyasa sun fara yunkurin yiwa mutanensu rajista ba akan ka’ida ba.
Ganin ce-ce-ku-cen da aka fuskanta a ranakun farkon kaddamar da rajistar zabe a jihohin Maradi, Damagaram, Diffa da Yamai ne ya sa hukumar zabe ta kasa kiran taron masu ruwa da tsaki a sha’anin zabe da nufin jan hankulan bangarorin siyasa game da hukuncin da ka iya hawa kan duk wanda aka kama da yunkurin rashin bin ka'ida.
Wani bidiyon da aka yada a kafafen sada zumunta a makon jiya na zargin kusoshin jam’iyar PNDS mai mulki da buga takardun haifuwa a boye a garin Damagaram, da nufin cimma wani buri a yayin rajistar dake gudana a yanzu haka, to sai dai sakatarenta mai kula da harkokin zabe Boubacar Sabo na cewa babu kamshin gaskiya a wannan batu.
Yanzu haka wasu ‘yan siyasa na cigaba da kalubalantar hukumar zaben ta CENI saboda yadda suke mata kallon mai raunin.
Domin kaucewa fuskantar matsalolin da yayi fama da su a zangon farko na rajistar zabe hukumar zabe ta bayyana daukar matakan tabbatar da tsaro a yankunan da ke fama da tashin hankula.
Mutane sama da miliyon 3 ne hukumar ta CENI ta ce sun yi rajistar zabe a yankunan Tilabery, Tahoua, Agadez da Dosso, yayinda tace za ta dauki matakan tace sunayen mutanen da suka yi rajista fiye da 1.
A saurari rahoton Souley cikin sauti daga birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar.
Facebook Forum