Zanga zanga da aka gudanar a birnin Kwanni ta kunshi ‘yan siyasa, sarakuna, malamai, ‘yan boko, ma’aikata, kungiyoyin farar hula da sauransu. Sun yi tururuwa ne a ajerin gwanon yin Allah wadai a yunkurin juyin mulki da kuma yunkurin hallaka shugaban kasa a cikin wannan watan. Yanzu haka dai ana tsare da sojoji da ake zargi da wannan yunkurin.
A cikin hirarsu da Sashen Hausa, Alhaji Zakari Umaru Dan majalisar dokoki, wanda kuma shine shugaban rukunin ‘yan majalisa da jam’iyar PNDS Tarayya, mai wakiltar birnin Kwanni, yace yunkurin juyin mulki koma baya ne a damokaradiyar kasar.
Sai dai a nasu bangaren ‘yan hamayya sun bayyana cewa, basu ga wani abu ba da yayi kama da kare damokaradiya a wannan zanga zangar. Bisa ga cewarsu, kamata ya yi a ba kowa irin wannan damar, ta bayyana ra’ayi amma ba bangare guda kadai ba.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Haruna Mamman Bako ya aiko daga birnin Kwanni, Jamhuriyar NIjar.