A jamhuriyar Nijar, duk da korafe korafen da jam’iyun hamayya ke nunawa akan kura-kuren da suka ce sun dabaibaye ayyukan rajistar zabe hukumar rajistar ta mikawa hukumar zaben kasar sabon kundin dake kunshe da jerin sunayen mutanen da suka cancanci kada kuri’a a zabubukan da za yi a farkon shekarar 2016.
Daga cikin ‘yan jamhuriyar Nijar mutane miliyan goma sha bakwai da ‘yan kai na yawan al’ummar kasar, mutane miliyan biyar da dubu dari da sittin da tara, da sittin da tara ne ke da izinin kada kuria a zabubukan da za a fara gudanarwa daga ranar ishirin da daya ga watan Fabrairu shekara ta dubu biyu da goma sha shidda a Jamhuriyar Nijar.
Shugaban watsa labarai na hukumar zabe Alhaji Kaso Salisu ya bayyana dalilansu na mikawa hukumar wannan kundi, duk da sukar da suke fuskanta daga ‘yan adawa.
Yace da za a yi masu adalci, da za a gane cewa aikin nan tare da ‘yan adawa suka yi shi tunda farko, in akwai wadansu kurakurai sun san dasu, in babu kuma sun sani. Yace kamata ya yi ‘yan adawa su karbi duk wani abinda aka yi sabili da wakilansu aka yi shi.
Shugaban watsa labaran yace an shafe sama da shekara daya ana fadi tashin gyaran kundin tsarin zaben kuma sun mikashi ga hukumar da aka ba nauyin tsara zabe, wadda a nata bangaren ta alkawarta nazarinshi.
Tun a ranakun farkon fito da sakamakon wucin gadi na ayyukan gudanar da zaben, ‘yan adawa suke zargin cewa kundin yana cike da kurakurai. Bisa ga cewar ‘yan adawa, kundin bashi da wani muhimmanci ga ‘yan kasa. Suna korafin cewa, an bukaci a gabatar da kundi da kowa ya yarda da shi amma a karshe aka yi akasin haka.
Ga cikakke rahoton da wakilinmu Suleman Mummuni Burma ya aiko daga Jamhuriyar Nijar.