A yayin da a yau litinin dalibai ke addu’o'in tunawa da wasu abokansu da jami’an tsaro suka bindige a yayin zanga zangar ranar 9 ga watan Fabarairun shekarar 1990 kungiyar dalibai ta kasa wato USN ta jaddada aniyar ci gaba da gwagwarmayar ganin an gudanar da binciken da zai bada damar zakulo masu hannu a wannan ta’asa don gurfanar da su a gaban shari’a.
Dubban dalibai ne suka hallara a dandalin da ake kira Place des Marthyrs da ke birnin Yamai a ranar litinin domin tunawa da dalibai 3 da suka kwanta dama bayan da jami’an tsaro suka bude masu wuta a lokacin wata zanga zangar tayar da mahukunta daga barci game da matsalolin daliban a lokacin.
Shekaru 30 bayan faruwar wannan al’amari, har yanzu ana ci gaba da jan kafa wajen gudanar da binciken da zai bada damar hukunta masu hannu a wannan kisa to amma a cewar sakataren kungiyar dalibai ta USN Idder Algabit, gaskiya za ta bayyana ko ba jima ko ba dade.
A shekarar 2017 ma wani dalibi ya rasa ransa a lokacin da jami’an tsaro suka kutsa jami’ar Yamai a yayin da daliban ke shirin gudanar da wata zanga zanga.
Dukan gwamnatocin da suka gabata a Nijer har zuwa wadda ke ci a yau, sun sha alwashin hukunta masu hannu a kisan daliban wato Abdou Maman Saguir, da Issaka Kaine, da kuma Alio Nahantsi to amma har yanzu hakar kungiyar daliban ta USN ta kasa cimma ruwa duk kuwa da cewa zanga zangar ta ranar 9 ga wata Fabarairun 1990 ta taimaka wajen mayar da wannan kasa akan tafarkin dimokradiyya.
A saurari labari cikin sauti daga birnin Yamai a Nijar.
Facebook Forum