Jiya litinin,shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sanya hanu kan tsarin mulkin mulkin Najeriya da aka yi wa kwaskwarima,hakan ya bai harkokin zaben shugaban kasa da na wakilan majalisa da gwamnoni daza’a yi cikin watan Afrilu karfin doka. A kwaskwarimar da wakilai suka yi wa tsarin mulkin sun karato da zaba zuwa watan janairu,amma bayan da humkumar zabe ta yi kukan lokacin bai wadatar ba,suka gyara dokar da ta daga zaben zuwa watan Afrilu.
Jaridar Wall Street Journal ta nan Amurka ta buga labarin cewa dubban wakilan zabe na jam’iyya mai mulkin Najeriya PDP ne suke haramar kada kuri’a a zaben share fage na jam’iyyar Alhamis din nan ga mai rai,wadda zai bude dandalin hada hadar zabe a kasa da ta fi yawan al’uma a nahiyar Afirka.
A zaben na PDP za’a kara ne tsakanin shugaba Jonathan da Alhaji Atiku Abubakar,tsohon mataimakin shugaban kasa,kuma tsohon baturen kastam.
Jiya litinin,wata kotu a Abuja, ta yi watsi da karar da wasu ‘yan PDP uku suka shigar na kalubalantar takarar Goodluck Jonathan a zaben share fage.
Alkali Ishaq Bello na babban kotun Abuja a hukuncinsa yace karar dake zargin tsayawar Jonathan ya kaucewa tsarin mulkin jam’iyyar,anyi riga malam masallanci,a bari sai bayan zaben share fagen.
Tsarin mulkin PDP ya yi tanadin shirin karba karba tsakanin kudanci da kuma arewacin Najeriya. Shugaba Jonathan ya fito ne daga kudancin Najeriya.