Wani sabon rikici ya barke a Jos babban birnin jihar Plateau wanda ya yi sanadin rasa rayuka da kaddarori. Kwamishinan yan sandan jihar Abdulraham Akanwo ya tabbatar da aukuwa lamarin wanda ya danganta da bangar siyasa da kuma kwantan bauna da aka yiwa wadansu dake kan hanya zuwa bukin aure.Shaidu sun ce an yi kone kone da asarar rayuka yayinda mutane da dama suka rasa rayukansu a harin, sai dai kakakin 'yan sandan bai tabbtar da asarar rayukan. A halin da ake ciki kuma, jami'ai a Najeriya sun ce an kashe a kalla mutane biyu da dama kuma suka jikkata a wani hari da aka kaiwa magoya bayan wani dan siyasa a yankin Niger Delta mai arzikin man fetir. Yan sanda sun ce Timi Alabie ya tsallake rijiya da baya lokacin da 'yan bindiga suka kaiwa gidansa hari a Opokuma cikin jihar Bayelsa. Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce an kama mutane da dama dangane da lamarin.
Wani sabon rikici ya barke a Jos, babban birnin jihar Plateau wanda yayi sanadin asarar rayuka da kaddarori.