Direbobin motocin tankunan jigilar man fetur a Nigeria sunjanye yajin aikin da suka soma bayanda hukumomi suka kama wani soja da ake zargi da laifin kasha wani direban tanker. Tun jiya ma ‘yan kungiyar NUPENG ta ma’aikatan man fetur da gas ta Nigeria suka bayyana niyyarsu na janye yajin aikin bayan zaman tattaunawar da suka yi da ministan kwadago na kasar Emeka Wogu inda suka zanta gameda kuntatawa da cin mutuncin da suka ce sojoji sun dade suna yi musu. Minista Wogu yace yanzu haka gwamnati na nan tana tattauna irin diyyar da za’a bayar ga iyalan shi wancan direbanm da sojan suka hallaka.Yajin aikin da direbobin tankokin suka yin a dan gajeren lokaci dai ya janyo dogayen layukkan mai a gidajen mai barkattai na Nigeria, tun ma ba a Lagos ba.
Direbobin da suka fara yajin aiki ranar litinin,sun dauki matakin ne bayanda suka zargin wani jami'in tsaro ya kashe wani dan kungiyar.