Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jadawalin zaben najeriyana 2011


Hoton mai neman tsayawa takarar shugaban kasa ma jam'iyyar PDP a Najeriya, Atiku Abubakar, a gefen wata hanya a birnin Lagos.
Hoton mai neman tsayawa takarar shugaban kasa ma jam'iyyar PDP a Najeriya, Atiku Abubakar, a gefen wata hanya a birnin Lagos.

Hukumar zaben Najeriya ta ce za a gudanar da zabubbukan shekara mai zuwa ta 2011 a cikin watan Afrilu, kuma za a fara ne da na 'yan majalisar dokokin tarayya

Hukumomin zabe a Nigeria sun bada jadawalin zabukkan da za’a a watan Afrilun shekara mai zuwa. Hukumar zaben kasar tace zaben ‘yanmajalisun dokokin tarayya za’a share fage da shi ran 2 ga watan na Afrilu, daga nan sai na shugaban kasa a ran 9, kana a kamala da na gwamnoni da na ‘yanmajalisun jihohi a ran 16 ga watan Afrilun. A da, cikin watan Janairu aka nemi a yi zabukkan amma sai hukumar zabe ta INEC ta nemi karin lokaci don yi wa rajistar masu jefa kuri’a kwaskwarima da sauran gyare-gyaren fuska ga shirin zaben. Jadawalin zaben da aka sako ya nuna cewa makkoni biyu za’a yi ana gudanarda rajistar masu zabe daga ran 15 ga watan Janairu, to amma hukumar zaben tace jam’iyyu na iya soma shirya zabukkansu na fitarda ‘yan takaransu daga ran Jumu’ar nan mai zuwa ma, in suna so.

XS
SM
MD
LG