Gwamnatin jamhuriyar Niger, tace tayi kuskuren kama mutane hamsin da tara bisa zargin cewa, su yan kungiyar Al Qaida ne bayan wata mumunar arangamar da aka yi a watan jiya. A ranar juma’a gwamnan jihar Agadez Garba Maikido ya nemi gafarar wannan kuskure a wani jawabi daya gabatar ta gidan talibijin, yana mai fadin cewa mutane hamsin da tara din yan gudun hijira wadanda suka yi kokarin yin smogal din kansu zuwa cikin kasar.
A watan jiya Niger ta kama mutane hamsin da tara a wani yanki mai tsaunuka na arewacin kasar. A lokacin jami’ai, sunce arangamar da aka yi da yan yakin sa kan kungiyar Al Qaida ta kashe yan yakin sa kai guda uku da soja daya.
Sai kuma gashi yanzu kuma, jami’an Niger suna fadin cewa an kama mutane ne a sakamakon wata gardama da direban dake tuka motar dake jigilar yan gudun hijira, wanda shi kam an kashe shi.
Kafofin yada labarun Niger sun bada rahoto cewa gwamnan Maikido da wasu jami’ai sunje har gidan direban da aka kashe suka nemi gafarar iyalinsa. Su kuma wadanda aka kama tuni har an sako su, kuma ana gudanar da bincike.