Mayakan gwamnatin wuccin gadin Libiya, sun kaddamar da abin da su ka bayyana da cewa shi ne “samamen karshe,” a kan birnin Sirte, daya daga cikin wurare kalilan das u ka rage a hannun tsohon Shugaba Moammar Gaddafi.
Jama’a na ta ficewa daga wannan gari na bakin gabar teku a lokacin da mayakan gwamnati wuccin gadin ke dannawa cikin unguwannin.
A jiya Litini, dakarun gwamntin wuccin gadin sun kwace wani sansani a ciki da wajen Sirte. Cikin wuraren das u ka kama hard a garin Qasr Abu Hadi, inda aka ce anan ne aka haifi Gaddafi cikin wata bukka irin ta makiyaya a ckin 1942.
Jami’an gwamnatin wuccin gadin Libiya sun sha alwashin sauka, bayan an kwace Sirte an kuma yi shelar nasarar kwace dukkannin kasar. Farayim Ministan wuccin gadi Mahmoud Jibril ya fadi jiya Litini cewa kwace Sirte da Majalisar Shugabancin Wuccin Gadin Libiya za ta yi zai sat a iya iko da dukkan yankunan tekun kasar, da na bisa tudu, da samaniya da ma tasoshin jiragen ruwa.
To amman yadda cewa za a cigaba fafatawa a ‘yan wasu wurare a can yankin hamadar da ke kudu, ciki hard a Bani Walid.