Saboda irin wannan cunkoson ne ya sa kungiyoyin kare hakkin bil'Adama suka gargadi hukumomi suyi wani abu a kai domin inganta yanayin rayuwar firsinoni musamman a wannan lokaci da ake fama da mugun zafi.
Malam Nasiru Seidu shugaban wata kungiyar kare hakkin bil'Adamawa yace duk gidajen kason dake kasar gado ne daga turawan mulkin mallaka. Akwai wasu da aka ginasu domin mutum dari biyu amma yau akwai dubu biyu ko fiye cikin kowannesnsu. Yace dole ne a samu matsala ta lafiya da matsalar yanayin rayuwa musamman dangane da zafin da ake fama dashi.
Ya cigaba da cewa akwai tsoffi da yara da mata cikinsu. Baicin haka akwai mara lafiya, ga kuma rashin tsafta saboda haka dole ne a fuskanci matsaloli.
Korafin 'yan rajin kare hakkin bil'Adama ya sa hukumomin shari'a sun danganta al'amarin da halin tsaikon da ake fuskanta a wajen harkokin tafiyar da shari'a a kasar ta Nijar.
Sai dai mai shigar da shari'a da sunan gwamnati yace matsalar ta samu asali ne daga rashin yawan ma'aikatan shari'a. Yana mai cewa domin tunkarar matsalar cunkoso ministan shari'a ya bada umurni a kafa kungiya ko hukuma da za ta shiga tsakanin 'yansanda da wadanda suka aikata kananan laifuka domin a daidaita maimakon a kai irin wadannan mutanen gidan kaso
'Yan rajin kare hakkin bil'Adama na ganin ba daidai ba ne a ce birni kaman Yamai mai jama'a fiye da miliyan daya gidan kaso daya gareshi.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Facebook Forum