Kwamitin Zartarwa na Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya a ranar Alhamis ya amince da shawarar da kwamitin Kwararru da Ci gaba ya gabatar, kan mai horar wa Augustine Eguavoen ya ci gaba da jagorantar Super Eagles a matsayin Koci,
A daren Alhamis hukumar kwallon kafar ta NFF ta fitar da wannan sanarwar.
Kwamitin har ila yau ya ba da shawarar cewa Eguavoen ya ci gaba da jagoranci tawagar a wasannin neman shiga gasar cin Kofin Nahiyar Afirka ta 2025 da za su fafata da Libiya a ranar 11 ga watan Oktoba.
Eguavoen, mai shekara 58, wanda ke rike da tawagar na wucin gadi, bayan ya jagorance su sau uku a baya, ya jagoranci zakarun Afirka sau uku zuwa nasara da ci 3-0 kan Benin da kuma kunnen doki ba ci da Rwanda a wasannin ranar farko da ta biyu a farkon watan Satumba
Eguavoen da tawagar fasaha mai ci yanzu, wadda ta haɗa da Fidelis Ilechukwu, Daniel Ogunmodede, Olatunji Baruwa da Tomaz Zorec, za su kuma jagoranci tawagar Super Eagles B a wasannin neman cancantar shiga gasar cin Kofin CHAN na shekara mai zuwa.
Dandalin Mu Tattauna