Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da ingantaccen tsarin fasfo na lataroni, ta yadda za a rika yin harkokin fasfo ta yanar gizo, domin ingantawa da kuma saukaka tsarin neman fasfo ga ‘yan Najeriya a cikin gida da waje.
Dama an dade ana kai ruwa rana a game da mastalolin nema ko sabunta fasfo a ofisoshin hukumar kula da shige da ficen Najeriya da ma ofisoshin jakadancin kasar a waje, inda yan kasar da dama ke kokawa a kan tsawon lokacin da ake dauka wajen samu sabon fasfo ko sabuntawa, zargin ma’aikata da rashin gudanar da aiki yadda ya kamata, zalinci a wajen aiki da dai sauransu.
Matsalolin dai sun kara ta’azara ne tun daga shekarar 2020 inda bidiyoyi kan yanayin da wasu yan Najeriya mazauna kasashen Larabawa, Amurka, Burtaniya, Jamus da dai sauransu ke ciki na rasa aiki da barazanar tasa keyarsu Najeriya sakamakon rashin iya sabunta fasfo dinsu a kan lokaci a ofisoshin jakadancin kasar a waje.
Saidai a watan Mayu, ma’aikatar harkokin cikin gida ta ce daga ranar 1 ga watan Yunin 2021 bada fasfo ga ‘yan Najeriya zai dauki tsawon makonni shida ne kawai, lamarin da ya ci tura sakamakon yawan ‘yan kasar da ke neman fasfo din a cewar wasu masu bukatar fasfo din.
Gwamnatin Najeriya dai ta kaddamar da tsarin fasfon yanar gizo a kasar Burtaniyya don inganta aikin da ake yi, kawo karshen masu damfarar yan kasar da sunan sama mu su fasfo da kuma rage wahalar da ‘yan kasar mazauna kasashen waje ke fuskanta, kamar yadda Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbeshola ya bayyana a yayin taron kaddamarwar.
Sabon tsarin fasfon yanar gizo da aka kaddamar yana da inganci da karıya. Musamman sai da lambar shaidar zama dan kasa na NIN wanda zai hana masu sace fasfon mutane anfani da shi, kamar yadda mukaddashin shugaban Hukumar Shige da Ficen Najeriya, Isa Jere ya bayyana.
Mataimakin jakadan Najeriya a kasar Burtaniya, Ambassada Sani Suleiman ya yi karin bayani a kan sabon fasfon yanar gizon a hira da Muryar Amurka, inda ya ce wannan tsarin “shi ne irinsa na farko a duk duniya.”
Ahmed Mohammed dan Najeriya mazaunin kasar Burtaniya; shi ma ya tofa albarkacin bakinsa da cewa wannan tsari na lataroni zai saukake matsaloli.
Gwamnatin Najeriya dai ta jaddada kudirinta na inganta tsarin neman fasfo ga 'yan Najeriya, yayin da ta kaddamar da sabon fasfo na intanet a kasar da Burtaniya, tare da cewa za a kafa tsarin a ofisoshin jakadancin Najeriya a kasashe sama da 100 nan gaba.
Saurari cikakken rahoton Halima AbdulRa’uf: