Sabon jami'in Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da Ebola Ould Sheikh Ahmed yace ya damu cewa saboda nasarar da ake samu wajen jinyar cutar Ebola, hakan yana iya janyo sakaci da ci gaba da yaki da cutar.
Wakilin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a yaki da wannan cutar, yayi magana da manem labarai jiya Laraba a Monrovia babban birnin Laberiya, a ziyararsa ta farko tun kama aikin zuwa yankunan da suke fama da wannan cuta.
Ahmed yace ra'ayinsa garwaye yake. Yace hakika har yanzu da sauran aiki kamin ace Laberiya ta rabu da cutar Ebola. A lokacinda yake kasar, jami'in ya gana da shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf.
Kasashen Laberiya da Saliyo da Guinea sune kasashen da cutar tafi yiwa barna.
Ahmed yace ya kamata yaki da Ebola ya kasance babban aiki da yake gaban gwamnati, domin al'amari ne da ya shafi mutanensu, da kuma makomar kasashen da suke yiwa jagoranci.