Hukumar kiwon lafiya ta duniya mai lakabin WHO tace zuwa yanzu annobar Ebola, ta kashe mutane dubu takwas da dari biyu da talatin da biyar a fadin duniya, tun barkewarta a yammacin Afirka.
Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta fada jiya laraba cewa a bara, mutane dubu 20, da 747 aka sani suka kamu da kwayoyin cutar. A Saliyo ne cutar tafi yin barna. Kamar yadda hukumar ta WHO tace, akwai alamun cutar ta dan lafa, duk da haka har yanzu a saliyo ne kasar da cutar tafi tsanani, domin ko a makon jiya zuwa hudu ga wata, an sami sabbin mutane 248 wadanda suka kamu da cutar.
Ahalinda ake ciki kuma, barayi a birnin San Pedro a Honduras, sun saki wata budurwa yar gwagwarmayar yaki da cutar kanjamau Karen Dunaway Gonzalez, yar shekaru 18 da haifuwa wacce ita ma kanta take fama da cutar. Sun rike na tsawon sa'o'i' takwas.
'Yan binidgar sun kamata ne tareda mahaifiyarta, amma suka sake uwarta bayan wani dan gajeren lokaci.
An ce 'yan binidgar sun saki wace suke garkuwa da ita din ne, bayan da uwarta Rosa Gonzalez tayi magana a kafofin yada labarai inda tace basu da kudi.