Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nasarar APC A Edo Ta Nuna Cewa Mutane Na Goyon Bayan Yadda Muke Tafiyar Da Tattalin Arzikin Najeriya – Tinubu


Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu)
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu)

Shugaban na Najeriya ya kuma yaba da yadda sauran ‘yan takara suka nuna dattaku yayin gudanar da zaben wanda ya ce an gudanar lami lafiya.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya Sanata Monday Okpebholo murnar lashe zaben jihar Edo da aka yi a ranar Asabar.

Okpebholo, wanda ya yi takara karkashin jam’iyya mai mulki ta APC ya samu kuri’u kuri'u 291,667. Sai dan takarar jam’iyyar PDP Asue Ighodalo wanda ya samu kuri'u 247,655.

Olumide Akpata, na jam'iyyar Labour Party (LP), ya kammala a matsayi na uku, inda ya samu kuri'u 22,763.

“Wannan nasara shaida ce cewa jama’a na goyon bayan jam’iyya mai mulki da manufofinta da kuma yadda muke tafiyar da tattalin arzikin kasa don kyautata rayuwar ‘yan Najeriya.” Kakakin Tinubu Bayo Onanuga ya ce cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Shugaban na Najeriya ya kuma yaba da yadda sauran ‘yan takara suka nuna dattaku yayin gudanar da zaben wanda ya ce an gudanar lami lafiya.

“Yin zabe cikin lumana kamar wanda aka gani a ranar Asabar ya nuna cewa Najeriya kasa ce da ke bin tafarkin dimokradiyya mai dorewa.

“Shugaba Tinubu na kira ga wadanda ba su gamsu da sakamakon zaben ba da su bi ta hanya da doka ta tanada don neman hakkinsu.” Onanuga ya ce.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG