Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Zata Iya Kawar Da Cutar Hanta Kwata Kwata Zuwa 2030


Ranar yau ce ranar tunatar da jama'a illar ciwon cutar Hanta a duniya kuma taken bana shine “Kawar da cutar Hanta daga doron kasa”.

Yau ranar ce da majalisar dinkin duniya ta ware a matsayin ranar cutar ciwon Hanta ta duniya wacce ake kira Hepatitis, bisa kididdigar da hukumar kula da lafiya ta duniya ta bayar akwai akalla mutane biliyan biyu masu dauke da cutar Hanta a fadin duniya, wanda daga ciki akalla mutane miliyan biyu na mutuwa sanadiyar cutar. taken ranar a bana shine “Kawar da cutar Hanta daga doron kasa”.

Masana nau’in cututtuka sun bayyana cewa cutar ciwon Hanta cutar ce babba mai kisa cikin ruwan sanyi da sauri wanda tafi cutar kanjamau kisan mutane cikin sauri.

Binciken na bayanin cewa akwai nau’in cutar ciwon Hanta guda biyar da suka hada da nau’in “A,B,C,D da E.”

A Najeriya, nau’in cutar ciwon ta Hanta na “A” ya bullo ne a jihar Borno, a garin Damasak, a ranar 3, ga watan Mayun, shekarar ta 2017, wanda ya zuwa ranar 2, ga watan Yulin 2017, aka bada tabbatatcen rahoto da kuma tsanmanin cutar har guda dari da arba’in da shida (146).

Kwararre akan sanin nau’in cututtuka dake asibitin kwararru dake Bauchi, Anas Muhammad Bello Dauda, yace wannan babban cuta ce wanda ke kisa cikin sauki abinda akasarin mutane basu gane ba domin cutar ce da mutun ka iya kamuwa da ita amma bai san cewa ya kamu ba saboda sanu a hankali take yiwa mutn illa.

Najeriya dai ta kudiri aniyar kauda cutar ciwon Hanta daga kwata kwata zuwa shekara ta 2030.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG