Jami'ar da ke kula da fanin bincike da wayar da kai akan yaduwar cututtuka, Dakta Chinwe Ochu ce ta bayyana wa manema labarai hakan a Abuja. Ta ce jihohin da za a bude dakunan gwajin sun hada da Ebonyi, Borno, Kano, Sokoto, Rivers, Filato da kuma Kaduna.
Dakta Chinwe ta kara da cewa hukumar ta lura babu inda ake gudanar da gwajin kwayar cutar COVID-19 a yankunan arewa maso gabas, da arewa maso yamma, da arewa ta tsakiya, da kuma kudu maso gabashin Najeriya, shi ya sa hukumar ta yanke shawarar daukar matakin cikin gaggawa.
Dakta Chinwe ta kuma ce baya ga gina wadannan wuraren, suna so mutanen dake zama a wadanan jihohin su dauki batun cutar da muhimmanci, su rinka sanar da hukuma wadanda ba su da lafiya da wuri domin a gwada su da wuri,ta haka ne kawai za a iya daukar matakan gwaji a kuma killace wadanda cutar ta riga ta kama su.
A halin yanzu dai, akwai dakunan gwajin cutar a jihohin Legas, Ibadan, Osun, Edo da kuma birnin tarayya Abuja.
Wannan mataki ya yi wa likitan iyali dakta Abu Yazid da ke zama a Abuja dadi, amma ya bada shawarar cewa kafin a kammala gine-ginen, a gaggauta horar da ma'akatan jinya da zasu yi aiki a wuraren domin samun nasarar dakile yaduwar cutar.
Da wannan sabon matakin na gwamnatin tarayya, dakunan gwajin zasu karu daga 6 zuwa 13. Kuma a cikin makonni 3 kacal ake sa ran kamalla gine ginen.
A saurari karin bayani cikin sauti.