Ministan lafiya a Najeriya, Farfesa Onyebuchi Chukwu, ya bayyana cewa, kasar ba zata iya cimma muradun karni ba muddar ba a dauki wadansu matakan gaggawa na shawo kan cutar dundumi da zazzabin ciwon sauro ba.
Ministan ya bayyana haka ne a birnin tarayya Abuja yayin wani taron shawo kan cutar dundumi da zazzabin cizon sauro a Najeriya. Ministan ya bayyana cewa, mutum daya cikin uku na ‘yan Najeriya yana cikin hadarin kamuwa da cutar, yayinda kasar ta kasance ta uku a duniya dake fama da cutar bayan Indiya da Indonesia.
Ministan ya ce, kashi 25% na mutanen dake rasuwa a Najeriya suna mutuwa ne sakamakon kamuwa da zazzabin cizon sauro, yayinda cutar ce sanadin mutuwar kashi 30% na mata masu juna biyu, kashi 11% kuma na kanannan yara.
Ministan ya jadada cewa, mata masu juna biyu da kuma kananan yaran da shekarunsu suka gaza biyar suna fuskantar barazanar kamuwa ko kuma mutuwa da zazzabin cizon sauro.
Bisa ga cewara ministan, Najeriya ta sami ci gaba ainun a cikin shekaru biyu da suka shige wajen kula da wadanda ke cikin hadarin kamuwa da cutar.
Farfesa Chukwu ya bayyana cewa, an yiwa gidaje dubu 103,262 feshin maganin sauro yayinda ake shirin yin feshi a gine gine dubu dari a karamar hukumar Nassara Eggon dake jihar Nassarawa a cikin shekarar nan ta 2012.