Wani bincike da aka gudanar tsakanin kasashen dake fama da talauci da kuma masu matsakancin karfin aljihu na nuni da cewa, kimanin matasa dubu uku ke kamuwa da kwayar cutar kanjamau kowacce rana.
An bayyana haka ne kwanan nan lokacin da shugabannin matasa daga kasashen duniya suka gabatar da shawarwari ga sakatariyar yaki da cutar kanjamau ta Majalisar Dinkin Duniya UNAIDS da za a yi amfani da su a yaki da cutar kanjamau daga yanzu zuwa shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.
Bisa ga rahoton, kimanin mata miliyan goma sha biyar zuwa ishirin da hudu ne ke dauke da cutar kanjamau a fadin duniya, sabili da haka kungiyar matasan mai suna CrowdOutAIDS ta gabatar da shawarwari shida ga sakatariyar UNAIDS.
Shawarwarin sun hada da karfafa kwarewar matasa a fannin shugabanci a dukan mataki a yunkurin wayar da kan jama’a da yaki da cutar kanjamau, da kuma hada hannu tsakanin matasan da sakatariyar UNAIDS.
An kafa kungiyar matasa ta CrowdOut AIDS ne da nufin cusa su cikin tsare tsare da kuma aiwatar da shirin yaki da cutar kanjamau musamman tsakanin mazauna yankunan karkara.