Tun shekara ta 2019 ne Najeriya da Kamfanin SIEMENS na kasar Jamus suka rattaba hannu akan wata yarjejeniyar yin aiki tare domin kara adadin karfin wutar lantarki dagaa megawat 4,500 da ake samu yanzu zuwa megawat 7000 kafin shekara mai zuwa kamar yadda babban mai ba Ministan Makamashi shawara a harkar samar da wutan lantarki Idris Mohammed Madakin Jen ya bayyana wa Muryar Amurka a Abuja.
Alhaji Idris ya ce Ministan ya yi hobbasa wajen ganin wanan aiki ya fara kuma ya yi tsayin daka akan ganin an kammala aikin kafin shekara mai zuwa saboda a cika wa shugaba Buhari burin sa na samar wa kasar da isassar wutar lantarki da akalla mutane miliyan 60 za su mora akai-akai.
Madakin Jen ya ce za a yi wannan aikin ne a karkashin shirin Shugaban kasa da ake kira PPI inda Najeriya za ta wakilci kamfanonin raba hasken wuttar lantarki da sauran masu ruwa da tsaki wajen saka hannun jari, wani abu da shugaban kungiyar Habbaka Matasan Arewa Imrana Nas ya ce an dade ana irin wannan alkawarin amma har yanzu akan batun wutar lantarki ta na kasa ta na dabo, inda ya bada tarihin cewa tun a shekarar 1999 ne ake gwagwagwa tsakanin mahukunta da yan kasa akan lamarin.
Shi ma mai fashin baki a al'amuran yau da kullum Comred Isa Tijjani ya ce in dai ba aikin aka yi aka gama ba, shi ba zai amince da romon baka ba, domin an dade ana ruwa kasa ta na shanyewa a kan batun samar da wutar lantarki.
Abin jira a gani shi ne yadda samar da wutar lantarkin zai kai ga farfado da masana'antun kasar da suka dade a kwance babu motsi.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti daga Madina Dauda:
Facebook Forum