Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Samu Karin Mutum 595 Da COVID-19 Ta Harba


Yayin gwajin rigakafin cutar coronavirus a birnin Seattle na Amurka
Yayin gwajin rigakafin cutar coronavirus a birnin Seattle na Amurka

Sabbin alkaluman da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta fitar sun nuna cewa an samu karin daruruwan mutane da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar.

A jiya Alhamis hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter wanda take sabunta alkaluman a kullum.

A cewar hukumar, mutum 595 ne cutar ta harba a ranar Alhamis 16 ga watan Yuli, wanda hakan ya mayar da adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar zuwa 34,854.

Hukumar ta kuma bayyana cewa mutum 14,292 ne suka warke daga cutar yayin da mutum 769 suka mutu.

An samu sabbin alkaluman ne daga jihohi 24 kuma har yanzu jihar Lagos ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar ta coronavirus, yanzu ta sake samun mutum 156. Sai jihar Ondo da ke bin ta da mutum 95.

Sauran jihohin da aka samu karin wadanda suka kamu da cutar sun hada da Rivers-53, Abia-43, Oyo-38, Enugu-29, Edo-24, Abuja-23, Kaduna-20, Akwa Ibom-17, Anambra-17, Osun-17, Ogun-14, Kano-13, Imo-11, Delta-6, Ekiti-5, Gombe-4, Plateau-4, Cross River-2, Adamawa-1, Bauchi-1, Jigawa-1, Yobe-1.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG