Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Lashe Kofin 'Yan Kasa Da Shekaru 17


짐바브웨 군사 쿠데타 1주일 만에 37년간 집권한 로버트 무가베 대통령이 사임했다. 수도 하라레의 국제컨퍼런스센터에 모인 시민들이 벽에 걸려있던 무가베 전 대통령의 사진을 내리며 환호하고 있다. 
짐바브웨 군사 쿠데타 1주일 만에 37년간 집권한 로버트 무가베 대통령이 사임했다. 수도 하라레의 국제컨퍼런스센터에 모인 시민들이 벽에 걸려있던 무가베 전 대통령의 사진을 내리며 환호하고 있다. 

Najeriya ta sake lashe kofin gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 17 bayan da ta doke abokiyar karawarta Mali da ci 2-0 da ake yi a Chile a karkashin kulwara hukumar FIFA.

Dan wasan Golden Eaglet Victor Osimhen ne ya fara zirawa Najeriya kwallonta kana jim kadan Funsho Bamgboye ya kara wata kwallon.

Gabanin zira kwallayen, Najeria ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida wanda Osinachi Ebere ya buga ya zubar.

Dan wasan Najeriya Osimhen shi ne dan wasan da ya lashe kyautar wanda ya fi zira kwallaye a gasar da kwallaye goma, wanda ba a taba samun dan wasan da ya yi haka a baya ba.

Wannan shin ne karo na biyar kuma da ‘yan wasan Golden Eaglet ke lashe wannan kofi kuma Najeriya ce kasa ta biyu da ta taba lashe kofin sau biyu a jere.

Baya ga haka wannan shi ne karo na takwas da Najeriya ke kaiwa ga wasan karshe a wannan gasa.

A shekarar 1985 Najeriya ta fara lashe kofin gasar a lokacinmulkin Shugaba Muhammadu Buhari ya na mulkin soja.

Waklin Muryar Amurka, Murtala Faruk Sanyinna ya mana dubi kan tarihin yadda Najeriya ta lashe gasar sau biyar:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG