Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Dage Haramcin Amfani Da Twitter


Tambarin Twitter
Tambarin Twitter

A ranar 5 ga watan Yunin bara, Najeriya ta haramta amfani da dandalin wanda ta zarga da taimakawa wajen ta da husuma a kasar.

Hukumomin Najeriya sun dage haramcin da suka kakabawa kamfanin sada zumunta da muharawa na Twitter.

Wata sanarwa da mai taimakawa shugaba Muhammadu Buhari a fannin kafofin yada labarai na zamani Bashir Ahmad ya fita ta ce, gwamnati ta dauki wannan mataki ne bayan da Buhari ya amince.

A ranar 5 ga watan Yunin bara, Najeriya ta haramta amfani da dandalin wanda ta zarga da taimakawa wajen ta da husuma a kasar.

Ko da yake, hana amfanin da shafin ya biyo bayan goge wani sakon Shugaba Buhari da Twitter ya yi a dandalin.

A cewar Ahmad, Shugaban kwamitin sasanta tsakanin Najeriya da kamfanin Twitter wanda shi ne shugaban hukumar NITDA, Kashifu Inuwa ne ya sanar da wannan sabon mataki.

Matakin zai fara aiki ne da misalin karfe 12 na dare agogon Najeriya a cewar Ahmad.

“Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da dage matakin dakatar da Twitter a Najeriya wanda zai fara aiki daga 12 na safe a ranar 13 ga watan Janairun 2022.” Sanarwar ta Ahmad ta kara da cewa.

XS
SM
MD
LG