Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Amince Da Yin Shafin Manhajar Sa Ido Kan Ayyukan Manyan Titina


Ministan ayyuka da gidaje na Najeriya Babatunde Fashola ne ya bayyana hakan a Abuja inda ya ce an amince da yin manhajar yanar gizo ta zamani da za ta bada dama a rika kula da ayyukan kwangilolin kan titina da kuma sa ido kan titinan su kansu.

Ministan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Abuja inda ya ce gwamnati ta bayar da kwangilar aikin shafin manhajar akan naira miliyan 203,845,333.50.

Fashola ya ce ya na sa ido akan ayyukan hanyoyi da gadoji dari 700 da ya ke ganin wannan fasaha za ta samar da tsarin da zai sa ido kan ayyukan titina da kuma ingancin ayyukan, ya kara jadadda cewa wannan sabon shafin manhajar fasahar na ICT, zai zama kamar wani tabaran hangen nesa ta yadda gwamnatin tarayya za ta rinka kula da ayyuka da kuma sa ido kan titinan kasar.

To sai dai kwararre a tsangayar diflomasiya ta kasa da kasa kuma mai sa ido a harkar gudanar da mulki a jami'ar Baze da ke Abuja, Farfesa Usman Mohammed, ya yi tsokacin cewa mataki ne mai kyau, amma me ya sa ba a kirkiri wannan mahajar ba tun tuni sai yanzu, ya kara da cewa duk dan Najeriya ya san irin hanyoyin da ake da su a kasa da yadda aka bada kwangilar su amma ba a gama su ba.

Farfesa Usman ya ce har yanzu hanyar Kaduna zuwa Kano an gagara sanin dalilin rashin aiwatar da kwangilar ta tsakanin manyan jami'an gwamnati, da 'yan majalisar kasa da ma 'yan kwangilar. Kamata ya yi gwamnati ta fito da hanyoyin da za a bi diddigin kudaden da ake warewa don kwangilolin hanyoyi a kasa, a cewarsa.

Shi ma shugaban kungiyar muryar talaka a shiyar arewa maso gabashin Najeriya Saleh Bakoro Sabon Feggi Damaturu, ya ce yunkurin ya na da kyau domin zai ba 'yan kasa damar sanin inda kudaden su na kasa ke tafiya kuma zai kara wa gwamnati farin jini amma fa in an bi tsarin da gaskiya.

To sai dai kwararre a fanin kimiyar gina hanyoyi Injiniya Rabi'u Sa'idu Sufi, ya yaba da wannan yunkuri na gwamnati saboda a ganinsa shugaban kasa da jami'an gwamnati za su samu sauki wajen sa ido akan ayyukan da ake yi a kasa kuma zai sa a samu ci gaba a kasa wajen wayar da kawunan jama'a da ke yawan korafin cewa an yi ayyuka a wasu sassa amma ba a yi a wasu ba.

Babatunde Fashola ya ce za a samu mutane 36 masu kula da manhajar a jihohin kasa tare da darektoci 6 masu wakiltar shiyoyi 6 na kasar.

Saurari cikkaken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00


TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG