Yayin matsalar garkuwa da mutane don neman kudin fansa ta zama babban dillanci a Najeriya, hakan ya sa hanyar zirga-zirga ta mota ya ragu, hada-hadar jirgin kasa kuma ta habaka.
Mutane kan yi dandazo a tashar jirgin kasa domin neman tikiti sakamakon wahalar da ake sha kafin a samu, wanda har ya sa ma’aikatan suka sauya jadawalin yadda za’a rika karbar tikitin jirgin.
Wani matafiyi ya ce sufurin jirgin abu ne da ya kamata ya kawo sauki, amma kuma sai aka samu akasin haka.
Sai dai wata mai hawa jirgin, Amina Gani, ta ce ma’aikatan tashar jigin suna bukatar horo na musamman don tafiyar da aiki yadda ya kamata.
A daya gefen kuma, kokarin da ake yi na shawo kan matsalar tsaro da garkuwa da mutane, rundunar sojin Najeriya ta ce ta tura jami’anta jihohin Kaduna, Katsina da Zamfara domin samar da tsaro.
Saurari cikakken rahoton Hauwa Umar daga Abuja:
Facebook Forum