Tattaunawar ministocin ta mayarda hankali ne akan batun sha'anin horo da amincin sayarda makamai da suka samu kyakyawar fahimta a kansu da nufin shawo kan barazanar ta'adanci da ya yi sanadiyar asarar dubban rayuka musamman a arewa maso gabas da wasu kauyukan Kamaru dake bakin iyaka.
Ministan tsaron Najeriya Janar Mansur Dan Ali mai ritaya ya waiwaye inda yarjejeniyar ta samo asali. Yace idan ba'a manta ba tunda Shugaba Buhari ya kama mulki ya je kasashen yankin tafkin Chadi dake makwaftaka da Najeriya saboda samun hadin kai na yadda za'a yi a kawo karshen bala'in Boko Haram da ya addabi kasashen musamman Najeriya.
Yace yarjejeniyar da kasar Faransa ta tanadi horas da sojojin Najeriya da batun tattara labarain leken asiri. Hadin kan sojojin kasashen nan biyar na yankin tafkin Chadi ya sa ,yan Boko Haram ba sa iya ketarowa su yaki Najeriya kamar da.
Shi ma ministan tsaron Faransa ya bayyana jin dadinsa akan yadda kasashen suka amince da hadin gwuiwa wajen yaki da miyagun dake daidaita kasashen dake makwaftaka da juna. Ya jinjinawa sojojin hadin gwuiwar dake aiki a kan iyakokin kasashen..
Ganin irin illar da rikicin ya haifar musamman tsakanin makiyaya da manoma Sanata Malam Aliyu Wakili yace majalisar dattawa zata dauki mataki.
Ga karin bayani.