Jihohin Zamfara da Katsina na fama da barayin shanu tare da masu kashe mutane ba tare da hakkin shari'a ba.
Su ma jihohin tsakiya suna fama da barayin shanu da kashe kashe tare da rikici tsakanin makiyaya da manoma.
Gwamnatin Buhari ta sha alwashin shawo kan matsalolin inda shugaban kasa ma ya umurci sojoji da 'yansanda su yi farautar wadanda suke da hannu a kashe kashen mutane a jihar Enugu dake kudu maso gabas.
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina yace sun samu gagarumar nasara akan masu aikata wadannan ta'arnaki. Yace sun kwato shanu fiye da dubu goma sha biyar. Tumaki sun fi dubu ishirin tare da rakuma da jakai. Yace sun kafa kwamitin dake maidawa mutane shanunsu. Babu mota dauke da sa ko shanu ba tare da takardar izini daga kwamitin ba da zata wuce. Yace gwamnonin jihohi shida sun yadda su bada takarda iri daya.
Barayin shanu ne suka koma suna kama mutane suna garkuwa dasu domin neman fansa. Gwamna Masari yace basu kyale mutanen ba.
Kwamishanan labarun Katsina Hamza Barodo ya yi kari kan mutanen. Saboda da tsawon wani daji da ya kai har jamhuriyar Nijar yace babu mamaki idan akwai barayin mutane da na shanu da ba 'yan kasa ba.
A bangaren Fulani da rikici kan hadasu da manoma, Abubakar Suleiman na kungiyar Miyetti Allah, na nanata hanyar masalaha. Yace gwamnati ta yi alkawarin basu dazuka amma har yanzu ba'a tabbatar masu da dazukan ba. Su kuma manoma sun yi noma har wajen burtalin da shanu ke bi. Wani lokaci akan wucewar ne suke samun matsala da manoma.
Ga karin bayani.