Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan shi ne ya karanta wasikar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikawa Majalisar saboda neman izinin kara ciwo bashin dalar Amurka biliyan 6.1 domin ya aiwatar da kasafin kudin bana.
Kasafin kudin na bana dai ya samu gibin Naira triliyan 5.6 kuma kasafin ya ginu ne akan kudin gangan danye man fetura akan kudi dalar Amurka 45 sanan a canji Naira daya zuwa dala kuma, an canza dala daya akan Naira 379 ne.
Idan a aka canza yawan wanan kudi na dalar Amurka biliyan 6.18 a Naira zai kama Naira triliyan 2 da Naira biliyan 343.
Sanata Mohammed Sani Musa yayi bayanin hujjojin daukan bashin inda ya yi nazari yana cewa abinda ke gaban Majalisar Dokokin kasa a yanzu shi ne yadda za a buda hanyoyin samar wa talakan kasa abinci ta hanyar inganta tsaro, samar da taki saboda noma, gina makarantu, samar da magunguna a asibitoci da sauran kayayyakin more rayuwa saboda haka dole a ci bashi idan har za a yi wa talaka aiki.
Karin bayani akan: Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Amma ga kwararre a fanin Tattalin arziki a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria Forfesa Muntaka Usman yana ganin ko a halin kaka, cin bashi ba alheri ba ne ga kasar domin ko ba dade ko ba jima dole ne a biya wadannan basussuka kuma a halin yanzu babu abinda kasa ke sarrafawa sai man fetur kuma a yanzu kasuwar man ya karye sosai.
To sai dai ga Shugaban masu Rinjaye a Majalisar Dattawa Yahaya Abdullahi Abubakar wadannan kudade ba bashi ba ne, akwai amfanin su, saboda tun lokacin da aka yi kasafin kudin bana an yi shi da gibi har na Naira triliyan 5.6 saboda haka wadanan kudade su ne gibin da za a cike wajen aiwatar da kasafin, ba wai sabon bashi za a karbo ba.
Idan ba a manta ba, Ofishin Kula da Basussuka ya fitar da kididdiga cewa a yanzu haka ana bin Najeriya bashi har na Naira triliyan 84 ya zuwa karshen shekarar da ta shude.
Saurari cikakken rahoton a sauti: