Mutumin wanda ba a bayyana sunansa ba, na daya daga cikin mutane 100 da rundara sojin Najeriya ke nema ruwa a jallo.
“Tsaro abu ne da kullum ake inganta shi, ya dangana ne bisa yadda muka wayi gari muka samu kan mu a ciki.” in ji Shugaban Hukumar, Injiniya Sale Dunoma.
Zai dai a dauki wadannan matakan ne tare da hadin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki a harkar filayen jirage.
Koda yake kamfanonin jiragen saman na ikrarin cewa nauyin samar da tsaro ya rataya ne a kan hukumar ta FAAN da sauran kamfanonin tsaro.
“Hakkin duba fasinjoji yana kan hukumar da ke kula da tashoshin jirage ne, ba akan kamfanonin jirage ba.” Kyfatin Ado Sanusi na kamfanin Arik Airline ya ce.
Domin jin karin bayani, saurari rahoton Babangida Jibril da ya aiko mana daga Legas: