A shirin mu na mata, mu samu zantawa da Nabila Garba Magashi, matashiya yar jihar Kano, wacce ta karanci Biochemistry amma daga farko ta so ta karanci Likitanci ne. Bayan ta yi karatun share fagge sai ta samu canjin ra’ayi kamar yadda ta bada bayani.
Ta ce ko da ta fara karatun, bata fuskanci wata matsala ba sakamakon abinda ta yi sha’awa ne, daga baya kuma bayan kammala karatunta ta yi wa kasa hidima a jihar Kano inda ta koyar da dalibai.
Ta kara da cewa bayan kammala karatun, da yi wa kasa hidima, bata samu aiki ba hakkan ya sa ta koma makarata inda ta yi kwas din koyarwa wato Education, bayan haka shine ta samu aikin koyarwa a National Open University.
Daga nan kuma aka tura ta sashen Litattafai wato Library, a jami’ar iIimi mai nisan zango. Ta ce da aka tura ta fannin library sai ta ga kamar bai dace da karatun ta ba, don ta so ta zama malamar makaranta wacce zata koyar, ta kuma samu lokacin yin sana’oin ta.
Bata fuskanci wata matsala ba illa hakan, dalilin da ya bata damar komawa domin yin karin karatu ta fannin da ta fi so. Kuma yanzu tana abinda ta ke so a hannu guda, da kuma 'yan sana’o'in dogaro da kai.
Ga rahoton Baraka Bashir cikin sauti.
Facebook Forum