Watan jiya ne Janar Gilbert Diendere kwamandan dakarun dake gadin fadar shugaban kasar Burkina Faso ya kwace gwamnati ya kuma kulle shugaban kasar da firayim ministansa.
Kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka nan take ta yi watsi da juyin mulkin da yin barazanar mayarda kasar saniyar ware idan bai mayar da mulki hannun gwamnatin farar hula da ya hambarar ba. Tawagar shugabannin ta tafi kasar inda ta tilastawa sojojin su sauka.
Bayan sojojin sun mika mulki sai kuma suka ki su mika makamansu lamarin da ya sa sauran sojojin kasar suka yiwo ca. Ganin hakan madugun 'yan tawayen ya arce zuwa ofishin jakadancin Paparoma inda ya nemi mafaka.
Jiya Alhamis Janar Gilbert Diendere ya mika kansa ga gwamnatin rikon kwaryar kasar bayan cimma daidaito da jami'an gwamnati a birnin Ougadougou fadar gwamnatin kasar.
Muryar Amurka sashen Faransanci ta ruwaito cewa Janar Diendere ya samu tabbaci ba za'a kasheshi ba. Amma shi da sojojin da suka yi juyin mulki ranar 16 ga watan jiya zasu fuskanci shari'a wadda za'a yi masu da adalci.
Janar Diendere ya fake ne a ofishin jakadancin Paparoma ranar Larabar makon jiya yayinda sojojin kasar suka yi yunkurin tilasta ma su 'yan tawayen su ajiye makamansu.