Dan bindigar da ake tuhuma da kashe mutane 12 da raunata wasu 58 a wani gidan sinima dake Jihar Colorado a nan Amurka, zai bayyana a karon farko gaban wata kotu yau litinin.
Hukumomin kurkuku, su na tsare da James Holmes shi kadai cikin wani daki a garin Aurora dake kusa da birnin Denver a Jihar Colorado.
Ana zargin Holmes da laifin jefa barkonon tsohuwa cikin dakin sinima da tsakar dare, lokacin da ake nuna sabon fim din nan na Batman mai suna "The Dark Night Rises." daga nan kuma sai ya bude wuta a kan masu kallon fim din. 'Yan sanda sun kama shi a wurin ajiye motoci na wannan gidan sinima ba tare da wata matsala ba.
A bayan da ya gana a kadaice da iyalan wadanda aka kashe da wadanda suka ji rauni jiya lahadi a garin Aurora, shugaba Barack Obama ya ce ya je shi can a matsayinsa na uba kuma maigida ba wai a matsayin shugaba ba. Ya ce kalmomi kawai ba zasu iya kwatanta irin wannan hasara ba, amma kuma kowa ya san irin ukubar dake tattare da yin rashi ta irin wannan hanyar.
Mr. Obama ya tabbatarwa da iyalan cewa akwai haske a karshen wannan yanayi mai duhu, kuma illahirin wannan kasa su na taya su juyayin wannan rashi.
Babu wani cikakken bayanin da ake da shi a game da wannan dan bindiga mai suna Holmes ko kuma dalilansa na kitsa wannan ta'addancin. An dai san cewa shi dalibi ne mai karatun digirin digirgir, ko PhD a fannin kimiyyar hanyoyin sarrafa sakonni na jikin bil Adama.
'Yan sanda sun gano kwamfutarsa a cikin gidansa wanda ya dasa nakiyoyi har guda sittin a ciki da nufin kashe duk wanda ya bude kofa ya shiga ciki.