Cibiyar Hana Yaduwar Cututtuka da Dakile su ta Amurka (CDC) ta ce ta aika wasu ma’aikatanta goma sha biyu zuwa wani birni na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo domin aiki kan cutar Ebola da ta abkawa yankin.
Barkewar cutar annobar, wadda ta fara shekara daya da ta gabata, yanzu haka ta kashe mutane sama da 1,800.
Cibiyar ta nuna cewa zata kara aikawa da karin wasu ma’aikata idan har tashin hanakalin da ake fama da shi na ‘yan bindiga a arewa maso gabashin yankin ya yi sauki.
A yanzu dai ma’aikatan hukumar CDC sha biyu ne aka tura zuwa can birnin na Goma, wanda shine babban birnin da matafiya suke yada zango a cikinsa wanda kuma yake kusa da iyakar Congo da Rwanda.
Hukumomin Birnin na Goma sun tabbatar da cewe mutum na 4 ya kamu da cutar ta Ebola.
Facebook Forum