Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum Miliyan 13 Ke Dauke Da Covid-19 a Duk Duniya


Tedros Adhanom Ghebreyesus, Shugaban hukumar lafiya ta WHO
Tedros Adhanom Ghebreyesus, Shugaban hukumar lafiya ta WHO

Adadin masu cutar coronavirus a fadin duniya ya kai miliyan 13 a cewar wata kididdiga ta kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Hakan na nufin cewa an sami karin masu kamuwa da cutar miliyan 1 a cikin kwanaki 5. Annobar ta kashe fiye da mutum dubu dari biyar a cikin watanni 6.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce Duniya ba za ta koma yadda ta ke a da ba nan kusa idan dai aka ci gaba da kaucewa daukar matakan kariya.

"Bari in fadi gaskiya, kasashe da dama basa yin abin da ya kamata, annobar kuma ta ci gaba da addabar al'umma," in ji shugaban na WHO, a wani taron manema labarai a shelkwatar hukumar a Geneva.

Ya kara da cewa "muddin ba'a dauki matakan da suka dace ba, wanda shi ne kadai hanyar kawar da cutar, to kuwa za ta ci gaba da habaka da kuma munana. To amma bai kamata a kai ga haka ba."

Kididdigar ta Reuters wadda ta dogara akan bayanan gwamnatoci, ta nuna cewa yaduwar cutar na kara habaka da sauri a yankin Latin Amerika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG