Ofishin kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Abuja, ya fitar da wata sanarwa da yammacin ranar Lahadi, cewa a kalla mutum 110 ne mayakan Boko Haram su ka yi wa kisar rashin imani, kana wasu da dama suka samu munanan raunuka a wannan hari.
MDD ta ce wannan kisar gilla aika aika ce kai tsaye a kan fararen hula da basu san hawa basu sauka ba, kana shi ne mafi yawa a cikin wannan shekara.
Shugaban ofishin Majalidar Dinkin Duniya a Najeriya, Edward Kallon, ya ce akwai yiwuwar masu ikirarin jihadin sun yi awon gaba da mata masu yawan gaske.
Tsohon shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Komred Isa Tijjani, ya ce alkaluman da MDD ta fitar babbar magana ce. Ya kara da cewa shugaban kasa baya sauraran kiran da ake masa a kan batun tsaro, dan haka talaka sai dai yasa addu’a, saboda rayuka mutane na cikin hadari. Ya kuma ce za su ci gaba da yin magana a kan sha’anin tsaro.
Da Muryar Amurka ta tuntubi masanin sha’anin tsaro Dr. Yahuza Ahmad Getso, a kan sabbin alkaluman, inda ya ce “hakan na tabbatar da sakaci da gazawa da kasawa da gajiyawa da rashin iyawa da rashin sanin ciwon kai da rashin kishin talakawan kasa irin na gwamnati.”
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da wannan aika aika a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi. Shugaban ya ce ya baiwa sojojin Najeriya dukkanin goyon baya na bukatar daukar matakan da suka kamata na kare rayukan ‘yan Najeriya.
Ga dai rahoton Hassan Maina Kaina: