Annobar cutar coronavirus na kara yaduwa a duk fadin duniya, ta kuma shafi mutane sama da miliyan daya.
A yayin da annobar cutar coronavirus ta shafi mutane sama da miliyan daya kuma take ci gaba da yaduwa a fadin kasashen duniya, Amurka kadai na da mutum 245,000 da suka kamu da cutar, adadin da ya fi na kowacce kasa a fadin duniya.
A yau Juma’a ake sa ran Fadar White House zata bada shawarar mutane su fara amfani da takunkumin rufe hanci da baki, don dakile yaduwar cutar a kasar, abinda a baya ta ce saka takunkumin ba zai kare mutum daga kamuwa da cutar ba.
Tuni magajin garin New York Bill De Blasio, ya bada shawarar mutane su dinga amfani da takunkumin rufe hanci da baki, ko kuma wani abu. Amma kada mutane su yi amfani da abun rufe hanci wanda likitoci ke amfani da shi, don a bar wa jami’an kiwon lafiya kadai su dinga amfani dasu.
Shi kuwa shugaban karamar hukumar Los Angeles Eric Garcetti, cewa yayi jama’a su dinga rufe hancinsu baki a duk lokacin da suke cikin taro.
Dr. Anthony Fauci, kwararren likita a fanin cututtuka masu yaduwa, mai ba shugaba Trump shawara, ya shaida wa gidan talabajin na CNN a daren jiya Alhamis cewa, bai san abinda yasa wasu jihohin Amurka basu kafa dokar hana zirga-zirga ba, a dai-dai wannan lokacin da annobar ke kara yaduwa.